Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya ce bayan kammala addu’ar uku a gidan tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari da ke Daura, shi da tawagar gwamnatin tarayya za su koma gidan gwamnatin Katsina domin ci gaba da karɓar gaisuwa daga baƙi masu zuwa.
Cikin wata hira da BBC, Gwamna Radda ya ce iyalan tsohon shugaban ƙasar za su ci gaba da zama a gidansa da ke Daura domin ci gaba da karɓar gaisuwa daga masoya da dangi.
”Amma mu za mu koma koma gidan gwamnati tare da tawagar gwamnatin tarayya, inda za mu shafe tsawon mako guda muna karɓar gaisuwa daga baƙin da za su zo”, in ji shi.
Tawagar gwamnatin tarayya da ke Daura ta ƙunshi ministoci kusan 22, ƙarƙashin jagorancin babban sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume.