Asusun bayar da bashin karatu na (NELFUND), ya amince da ƙarin wasu manyan makarantu 22 a faɗin ƙasar waɗanda za ta bai wa ɗalibansu bashin karatu.
Wannan ƙarin ya kawo adadin makarantun da suka shiga tsarin zuwa 108 kuma, kamar yadda NELFUND ya sanar a shafinsa na X.
Sanarwar ta ce, “Asusun bayar da bashin karatu na Najeriya ya sanar da cewa ɗalibai daga waɗannan ƙarin manyan makarantu 22 na jihohi za su iya neman bashin karatu.”
“Wannan ya biyo bayan wani nazari da kwamitin tantance ɗalibai ya yi.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya ɓullo da tsarin bayar da bashin bayan ya rattaba hannu kan dokar da ta kafa asusun, wanda yake samar da tsarin bayar da bashi ga ‘yan Najeriya marasa galihu ko masu ƙaramin ƙarfi domin sauƙaƙa biyan kuɗin makaranta.