Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPCL, ya sanar da cewa za a kaddamar da karin gidajen mai guda 100 a duk fadin kasar nan da watanni goma sha biyu masu zuwa.
Manajan Darakta na Kamfanin NNPC Retail Limited, Huub Stokman ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wajen bikin kaddamar da tashoshin CNG guda 11 a lokaci guda a fadin Abuja da Legas.
Ya ce CNG zai kasance mai rahusa kashi 40 bisa 100 fiye da Premium Motor Spirit, wanda aka fi sani da fetur ga ‘yan Najeriya.
“CNG za ta kasance mai rahusa kusan kashi 40 fiye da man fetur a Najeriya. Kuma tare da ci gaba da saka hannun jari, zai iya zama wani muhimmin sashi na cakuda makamashinmu.
“A cikin watanni 12 masu zuwa, Kamfanin NNPC Retail zai kaddamar da shafukan CNG sama da 100,” in ji shi.
Ku tuna cewa a watan Agustan 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin Shugaban Kasa na Compressed Natural Gas Initiative, PCNGI, domin dakile tasirin cire tallafin mai a watan Yunin bara.