Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa, kamar yadda Ministan Sufuri Sa’idu Ahmed Alkali ya bayyana.
Da yake magana yayin wani taron tuntuɓa tsakanin ‘yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar, ministan ya ce lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka kammala.
“Amma zuwa yanzu an kammala kashi 53 cikin 100,” in ji shi cikin wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labarai ta fitar a yau Laraba.
A 2024 gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗin da za ta kammala aikin daga wani bankin kasuwanci na ƙasar China, abin da ministan ya jaddada a yau din.