fidelitybank

Za mu kama masu amfani da tufafin jami’an mu – Sojoji

Date:

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce za ta fara kama mutanen da ke amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba.

Cikin wata sanarwa da kakain rundunar, Commodore A Adams Aliu ya fitar,ya ce tana gargaÉ—in mutane domin su fahimci abubuwan da doka ta tanada da kuma illar da ke tattare da amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba.

Matakin na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun yi zargin cewa wasu mutane waÉ—anda ba sojoji ba sanya tufafin sojojin ba tare da izini ba.

“Ya zama dole mu tunatar da jama’a cewa yin amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba laifi ne, kamar yadda sashe na 12, Æ™aramin kashi na 110 (1) da (2) na kundin aikata laifuka ya bayyana, laifi ne ga duk mutumin da ba ya aiki cikin rundunar sojin Najeriya, ya sanya tufafin sojoji ko wani abu da ke kama da tufafin,” in ji sanarwar.

Rundunar ta bayyana ƙarara cewa bin wannan umarnin na da matuƙar muhimmanci, kuma rashin bin umarnin na iya haifar da kamawa da kuma gurfanar da mutum a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada.

vanguard (nigeria)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp