Shugaban mayaƙan Hothi a Yeman ya ce, idan Isra’ila ba ta bari aka ci gaba da shigar da kayan agaji zuwa Gaza nan da kwana huɗu ba, ƙungiyarsa za ta dawo da hare-hare kan manyan jiragen ruwa a Tekun Maliya.
Ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Abdulmalik Al-Hothi ya jaddada matsayar ƙungiyar ga duniya baki ɗaya.
A farkon watan nan ne Isra’ila ta datse damar ci gaba da shigar da agaji yankunan Falasɗinawa a wani mataki na matsa wa Hamas lamba ta amince da buƙatar tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta.
A shekarar 2023 mayaƙan Hothi suka soma ƙaddamar da hare-hare kan jigaren ruwa da ke hada-hada tsakanin ƙasashe, a wani mataki da suka ce nuna goyon baya ne ga Falasɗinawa a Gaza