fidelitybank

Za mu kai El-Rufa’i kotu – Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Date:

Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta yi barazanar ko dai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya nemi afuwar ɗaliban shehin malamin kan rashin adalcin da ta ce ya musu, ko kuma su maka shi a kotu.

Wannan na ƙunshe a wata takarda da gidauniyar ta fitar, wadda Sayyadi Aliyu Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya sanya wa hannu, inda gidauniyar ta ce sun ba El-Rufai nan da zuwa ƙarshen watan Ramadan.

Sayyadi ya ce dole ne El-Rufai ya fito ya bayyana cewa ya yi laifi, “sannan ya nemi afuwar gidauniyar da ɗalibanta da ma jagoranmu.”

Takardar ta zargi El-Rufai ba ” jami’an tsaro umarni su samame a makarantun tsangayarmu. Sun je har gidan malaminmu, Sheikh Ɗahiru Bauchi suka kwashe ɗaliban makarantarmu masu karatun Qur’ani. Kuma har yanzu akwai ɗaliban da ba mu san inda suke ba.”

Sayyadi ya ƙara da cewa, “an yi samamen ne da gangan domin a tozarta Sheikh Ɗahiru Bauchi da ɓata aikin da ya ɗauki tsawon rayuwarsa yana yi na ilimantar da al’umma da tabbatar da zaman lafiya.”

Sayyadi ya ce idan har zuwa ƙarshen Ramadan El-Rufai bai fito ya bayar da haƙuri ba, “za mu kai ƙararsa wajen shugaban ƙasa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam da ma kotu domin a ƙwato mana haƙƙinmu.

“Idan kuma duka ba su yi mana adalci ba, za mu kai ƙararsa wajen Allah ta hanyar addu’o’i.”

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp