Ministan harlkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi bayani kan tattalin arzikin Rasha cewa za su jure takunkumim da aka ƙaƙaba musu.
Ya ce,”mun jure wa irin wadannan matsalolin ciki tarihin mu.”
Ya kuma ce “Tunani da nazarin Rasha zai inganta bayan wannan rikicin.”
“Ina tabbatar muku cewa, za mu jure wa komai, kuma za mu dauki dukkan matakan kauce wa dogara ga kasashen yammacin Turai, a dukkan fannonin rayuwar mu.”
Lavrov ya kuma ce rasha ta “janyo hankalin duniya” cewa Ukraine na juya ma Rasha baya na tsawon shekaru, kuma ya ce: “Ana mayar da Ukraine karen farautar kasashen yammacin Turai.”