A bayaninsa na farko a matsayin martani kan harin da aka kai a daren jiya, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce sai ya hukunta maharan.
Ya ce maharan sun so ficewa ta Ukraine amma an tsaurara jami’an tsaro a hanyar.
Putin ya ayyana gobe 24 ga watan Maris a matsayin ranar hutu domin jimantawa juna.
Putin ya ce duka maharan ana tsare da su yanzu. In ji BBC.


 

 
 