Muƙaddashin babban Sifeton ‘yan sanda na kasa Olukayode Adeolu Egbetokun, ya yi Allah wadai da wasu jami’an rundunar ‘yan sanda da suka tuƙa mota suka bi ta kan wani mutum a wani lamari da ya faru ranar Alhamis a jihar Edo da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce mukaddashin Babban Sifeton ‘yan sandan ya bayar da umarni ga jami’an ‘yan sandan – waɗanda yanzu haka ke tsare a Edo – da su hallara a shalkwatar hukumar da ke Abuja ranar Litinin domin ɗaukar mataki a kansu.
Cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga yadda jami’an ‘yan sandan suka tuka wata mota tare da bin ta kan wani mutum da ake tunani direban motar ne, da ya kwanta a gaban motar, lamarin da ya jefa mutanen da ke wajen cikin firgici.
Sanarwar ‘yan sandan ta yi kira ga al’umma musamman mutanen garin Ekpoma da su kwantar da hankulansu, tare da alƙawarta cewa rundunar ‘yan sandan ba za ta lamunci irin wannan mummunan aika-aika da wasu ɓata-garin jami’anta ke yi ba.