Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta ce ta fara daukar matakan ɗinke ɓarakar da ta kunno kai a tsakanin ‘ya’yanta.
Jam’iyyar dai ta ce tuni ta ɗauki matakin ladabtar da ‘ya’yanta da ta ke zarginsu da yi mata zagon kasa, da ya sa wasu ke mata kallon kyanwar Lami a fagen siyasar Najeriya.
Rikicin baya bayan nan da ya shafi jam’iyyar ta PDP, y asa wasu daga cikin jiga-jigan ta mayar da hanakali wajen sasanta ɓanagaren shugaban jam’iyyar Ambasada Umar Damagun da wasu ƙusohin jam’iyyar.
Wannan takun sakar dai, ya sa jam’iyyar ta rabu zuwa gida biyu. Inda bangren da ke goyan bayan shugaban jam’iyyar Umar Damagun ya dakatar da sakataren yada labaran jam’iyyar da mai ba ta shawara kan harkokin shari’a, yayin da shi kuma ɗaya ɓanagaren ya dakatar da Umar Damagun daga mukaminsa na ruƙo, inda suka maye gurbin sa da Yayari Muhammad.
Bala Muhammad shi ne gwamna jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP, ya ce suna nan kan bakar su na kowa ya tsaya a inda yake, za su duba yadda dokar jam’iyyar ta ce don ganin an sami daidaito a tsakanin yan jam’iyyar.
A ceewarsa ”Zamu yi kokari waje ganin an sami hadin kai a tsakanin yan jam’iyyarmu, musamman ganin yadda har yanzu al’ummar Najeriya, na ra’ayin jam’iyyar PDP mai albarka wadda kuma ita ce zata kawo masalaha a Najeriya tunda muna da ƙwararu, da masana makamar aiki da za su fitar da kasar daga halin da ta ke ciki”
Haka kuma ya ce “an kafa kwamiti karkashin Chief Tom Otimi, wanda za su ladabtar da ko waye ko wanene, ko wanda ya yi izgilanci, ko ya yi rashin kunya, ko tunƙaho da ya kai ga cin mutuncin jam’iyyar ko zarafin dan jam’iyya, komai girmansa, kuma ko waye shi, ko da kuwa ni ne” inji Bala Muhammad.
Haka kuma ya ce a halin da ake ciki yanzu sun ɗinke dukkan wata ɓaraka da jam’iyyar take fuskanta saboda irin matakan da suka ɗauka.
Jam’iyyar PDP ta sha fama da rikice-rikice tun daga kafuwarta a shekarar 1998, kimanin shekara 26 da suka gabata, tun tana da mulki, har zuwa barinta mulki.
Tun bayan kayar da PDP da APC ta yi a zaɓen 2015 ne aka fara samu matsala, inda jam’iyyar ta dare biyu a tsakanin shugabancin tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Maƙarfi da tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff.
Jam’iyyar yanzu ita ce babbar jam’iyyar adawa, wannan ya sa ake tunanin rikice-rikicen bai rasa nasaba da hanƙoron neman takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027.