Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce suna da kuduri na ganin sun haɗa kan ƙungiyar Ecowas.
Barau ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da BBC, inda ya ce ya zama wajibi Ecowas ta haɗa kai domin samun ci gaba da ya kamata.
“Kafin zuwan Turawa, ƙasashen Afrika ta Yamma ko Ecowas sun kasance ƙasa ɗaya. Ana yin Hausa a kowane yanki ka je kama daga Nijar, Mali, Ghana da sauransu haka ma ga duka sauran yaruka”.
“Bayan zuwan Turawa ne suka raba kawunanmu, kuma ya kamata mu haɗa kai yanzu,” in ji Barau.
Ya ce idan ana haɗe za a fi samun ci gaba, walwala da kuma jin daɗi na al’umma.
Mataimakin shugaban majalisar ta dattawa ya ce za su yi duk abin da za su iya wajen hada kan mambobin kungiyar ta Ecowas.
Ya kuma ce suna da kudurin ganin an samar da kudi bai-daya na kasashen.
Barau ya ce suna da kudurin kawo tsarin da zai kawo hadin kai ta hanyar tattalin arziki, tsaro da kuma ci gaban yankin.