Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce, gwamnatinsa ta fara yunƙurin gyara tsarin birnin jihar domin kiyaye jihar daga ambaliya.
Zulum ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ziyarar gani da ido da ya yi wajen gyara da ake yi a dam ɗin Alau, inda ya ce har yanzu akwai wasu da suke gini a magudanan ruwa da kuma masu zuba shara suna toshe magudunan ruwa.
“Za mu duba tare da gyara tsarin birnin Maiduguri domin mu tabbatar dukkan magudanan ruwanmu a buɗe suke kuma suna aiki,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi gargaɗin cewa duk wani gini da aka yi a magudunan ruwa za a rushe su.
Ya ce za su ɗauki matakin rusau ɗin ne domin kare sake aukuwar irin ambaliya da ta auku a ranar 10 ga watan Satumban 2024 a Jere da ke Maiduguri.
A game da fargabar da ake yi a Maiduguri na sake aukuwar ambaliyar, Zulum ya buƙaci ƴan jihar su kwantar da hankalinsu, inda ya ce akwai babbar ma’adana ta dam ɗin Alau ɗin, da ya ce za ta janye ruwan idan ya cika.