fidelitybank

Za mu gina wa ƴan Najeriya gidaje dubu biyar-biyar a kowace shiyya – Gwamnatin Tarayya

Date:

Gwannatin Tarayya ta ce, tana shirin gina gidaje dubu biyar-biyar a dukkan shiyyoyi shida na kasar, don bunkasa samar da gidaje.

Ƙaramin ministan gidaje da raya karkara na Najeriya Alhaji Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da BBC dangane da bikin ranar inganta wuraren zama da gidaje na wannan shekara.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɓullo da wannan rana ne da manufofi daban-daban ciki har da rage yawan tururuwar al’umma zuwa birane.

Gwamnatin Najeriya ta ce dama akwai wannan tsari na gina gidaje a ƙasar, amma kasancewar wannan ma’aikatar a baya tana ƙarƙashin ma’aikatar ayyuka da makamashi. Amma yanzu an cire ta daga nan kuma za ta fara aiki gadan-gadan.

“Muna da shirin gina gidaje dubu dai-dai a kowacce jiha. Muna jiran Shugaban ƙasa ya sahhale mana ne sannan mu ƙaddamar da aikin.

“Akwai tsarin bai wa waɗanda ba su da gata kyauta, wasu kuma a ba su cikin farashi mai sauki,” in ji T Gwarzo.

Ministan ya ce sun kammala tsare-tsare da zane-zanensu, iyakaci su ƙaddamar da wannan aiki nan ba da jimawa ba.

Ya ƙara da cewa aikin na da fuska biyu, na farko akwai wanda ake kira ‘Mega City’ wato manyan birane, shi ne za a gina gidaje dubu biyar a kowacce shiyya ta Najeriya.

Amma ya ce faruwar aikin ta ta allaƙa ne da gabatar da kasafin kuɗi wanda za a yi nan ba da jimawa ba.

Ka shi na biyu shi ne, na raya karkara, wanda za a je ƙananan hukumomi a yi hanyoyi a fitar da titi da kasuwanni ta yadda za su zama kai ɗaya da birane, kamar yadda ministan ya bayyana

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp