fidelitybank

Za mu fara buga sunayen Alkalan da suke hada baki masu safarar kwaya – Abba

Date:

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya yi gargadin cewa ba wai kawai gwamnatinsa za ta fara kai rahoton Alkalan Kotuna da ke hada baki da barayin miyagun kwayoyi ba, amma za su buga sunayensu a shafukan Jaridu domin fallasa yadda suke mu’amala da su.

Gwamnan, wanda ya bayyana mamakinsa da jajircewar wasu dillalan miyagun kwayoyi da ke neman hanyoyin da doka ta tanada domin a sako musu haramtattun kayan da aka kwace, ya ce gwamnatinsa a shirye take ta tunkari su da wanda ake zargi da hada baki da alkalan su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta cika da mamaki a yakin da take yi da yaduwar miyagun kwayoyi a jihar sakamakon ayyukan barayin da ake zarginsu da hada baki da alkalai.

Gwamna Yusuf ya ce ya gano cewa mutanen da ke sana’ar miyagun kwayoyi sun samu nasarar sayo umarnin kotu domin a sako musu haramtattun alkalan da ba su yi wa Kano dadi ba.

Dangane da wannan lamari mai cike da tada hankali, Gwamna Yusuf ya umurci babban mai shari’a na jihar da ya samar da cikakkiyar dabara don hana masu safarar miyagun kwayoyi yin amfani da baragurbin doka a jihar, tare da samar da hanyar da za a shawo kan lamarin.

Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin bangaren shari’a da gwamnati domin kare jihar daga hadurran da ke tattare da safarar miyagun kwayoyi.

Ganin yadda KAROTA ta himmatu wajen kamo miyagun kwayoyi, Gwamnan ya bukaci hukumar da ta dauki matakin da ya dace domin kawar da abubuwan da aka kwace.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp