Hukumar zaɓen Najeriya, INEC a bayyana aniyarta na fara amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen gudanar da ayyukan zaɓe a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun babban kwamishinta kuma shugaban kwamitin wayar da kai da yaɗa labarai, Sam Olumekun, ta ce hukumar fasahar za ta taimaka wajen sauƙaƙa wa hukumar ɗaukar matakai la’akari da bayanan da za ta samu ta hanyar fasahar.
”Haka kuma fasahar za ta ƙara ƙarfafa sahihancin zaɓuka ta hanyar tattara alƙaluma da kuma tantance aihinin alƙaluman zaɓe”, a cewar sanarar.
Tuni dai hukumar ta sanar da kafa sashen fasahar ƙirƙirarriyar basirar ta AI a ƙarƙashin ɓangaren sadarwar hukumar, domin fara inganta ayyukan fasaha na hukumar, tare da kawar da matsalolin da ake fuskanta da suka shafi fasahar sadarwa.
Hukumar ta ce a baya-bayan nan ta halarci tarukan duniya waɗanda ta ce an shirya kan tasirin fasahar AI kan zaɓukan ƙasashe