Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta nemi a ɗauki matakin kauce wa sake ƙona Ƙur’ani, ‘yan kwanaki bayan wani ya ƙona kwafin littafin mai tsarki a Sweden.
Ƙungiyar mai mamba 57 ta gana a birnin Jeddah na Saudiyya don lalubo martanin da za su mayar kan ƙona Ƙur’anin da Salwan Momika, ɗan asalin Iraƙi mai shekara 37, ya yi bayan ya tattaka shi a ƙofar wani masallaci a birnin Stockholm.
‘Yan sanda ne suka ba shi kariya kafin ya aiwatar da aniyar tasa, wanda ya ce ya yi hakan ne don ya nuna ‘yancinsa na faɗar albarkacin baki.
A yau Lahadi, Organization of Islamic Countries (OIC) ta shawarci ƙasashe mambobinta “su ɗauki matakin bai-ɗaya don guje wa afkuwar wulaƙanta Ƙur’ani”, kamar yadda wata sanarwa da suka fitar bayan taron ta bayyana.
“Dole ne mu ci gaba da tunasar da ƙasashen duniya game da aiwatar da dokokin ƙasa da ƙasa da gaggawa, waɗanda suka haramta nuna duk wata ƙiyayya ga addinai.”
Lamarin ya jawo zanga-zanga a faɗin duniya, inda ƙasashen Musulmi kamar Daular Larabawa da Moroko da Kuwait da Iraƙi suka kira jakadan Sweden don nuna ɓacin ransu.