fidelitybank

Za mu dauki matakin fansa a kan Sojoji 6 da aka kashe mana a Neja

Date:

Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin ɗaukan fansa kan kisan da aka yi wa sojojinta shida bayan yi masu kwanton ɓauna yayin da suka je jihar Neja domin aikin kwantar da tarzoma.

Sojojin sun je aiki ne ƙauyen Karaga a yankin Shiroro ranar Juma’a inda wasu da rundunar ta kira ƴan ta’adda suka kai masu hari.

Wata sanarwa daga rundunar sojin ta ce an kashe da dama cikin maharan sannan kuma ana neman wasu a cikinsu.

Rundunar ta yi alƙawarin ɗaukar fansa kan kisan sojojin.

Sojojin da aka kashe sun haɗa da manyan jami’an soji biyu da wasu sojoji huɗu, a cewar rundunar. Sojoji biyu sun ji rauni a harin.

Rundunar ba ta tabbatar da rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wani jami’in soji.

Babu ƙarin bayani game da waɗanda suke da hannu a harin amma ana zargin ƴan bindiga da hannu a kai wa jami’an tsaro hare-hare a baya-bayan nan.

Harin ya zo ne yayin da Najeriya ke karɓar baƙuncin taron yini biyu kan yaƙi da ta’addanci a Abuja, babban birnin ƙasar.

Harin kwanton ɓaunan ya so ƴan makonni bayan kisan sojoji 16 a lokacin da suke wanzar da aikin zaman lafiya a tsakanin wasu al’umomi da ba sa ga maciji da juna a jihar Delta.

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da suka shafi yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke kai hare-hare a sassan ƙasar sai dai hukumomi sun sha bayyana irin ƙoƙarin da suke na magance ƙalubalen da tsaron ƙasar ke fuskanta.

vanguard new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...

Tarayyar Turai tamince da ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da ƙaƙaba wa Rasha...

Gwamnan Filato ya zargi Jami’ai da kin kama ‘yan bindiga

Gwamnatin jihar Filato ta zargi jami'an sojojin ƙasar da...

Za a yi wa Buhari addu’a a Abuja

Gwamnatin Tarayya za ta jagoranci gudanar da taron addu'o'i...

Buhari ya ban umarni na kula da Talakawan Najeriya – Peter Obi

Jagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce,...

Sojojin hadin gwiwa sun hallaka ‘yan Boko Haram a tafkin Chadi

Rundunar hadin gwiwa mai yaƙi da Boko Haram a...

Na yi rashin aboki na gari kuma Najeriya ta rasa mutumin kirki – Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Tinubu, na ci gaba da alhinin...
X whatsapp