Ministan Sufuri, Sa’idu Alkali, ya bayyana aniyar Najeriya na magance matsalar da ke haifar da hayaki mai gurbata muhalli daga masana’antar sufuri.
Ministan ya yi wannan alkawarin ne a taron kolin COP28 da ke gudana a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin jama’a, Jamilu Ja’afaru ya fitar.
Alkali ya jaddada babban burin Najeriya na ba wai kawai yakar sauyin yanayi ba, har ma da fadada hanyoyin motsi ga dukkan ‘yan Najeriya, tare da mai da hankali akai kan tallafawa hanyoyin sufuri mai dorewa da karancin iskar Carbon.
Ministan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe wajen samar da masana’antar sufuri mai dorewa da juriya, yana mai jaddada alfanun da al’ummar kasar za ta samu.
Dangane da koma bayan da COP28 ke ci gaba da yi, furucin nasa wata shaida ce ga yunƙurin Najeriya na magance matsalolin muhalli, musamman a fannin sufuri.
“Wannan matsayi mai karfin gwiwa yana aiki a matsayin kira na hadin gwiwa da kirkire-kirkire, inda ya sanya Najeriya a sahun gaba na ci gaba mai dorewa a cikin masana’antar sufuri,” in ji shi.


