Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya ce za a dakatar da duk wasu ayyukan Hamas a Jamus, sakamakon harin da ba a taba ganin irinsa da kungiyar ta kai kan Isra’ila ba a karshen mako.
Bugu da kari, za a dakatar da kungiyar hadin kan Falasdinu ta Samidoun, in ji Scholz a wani jawabi da ya yi a gaban majalisar dokoki a Berlin a safiyar Alhamis.
Tuni dai Tarayyar Turai da Amurka ta ayyana Hamas a matsayin kungiyar ta’addanci.
Kungiyar Samidoun ta yi murna da harin da aka kai Isra’ila a ranar Asabar ta hanyar raba kayan zaki a gundumar Neukölln na Berlin.
“Wannan abin raini ne. Wannan rashin mutuntaka ne. Ya ci karo da dukkan dabi’un da muka sadaukar da su a matsayinmu na kasa,” in ji Scholz. “Ba mu yarda da kiyayya da tunzura jama’a ba tare da daukar mataki ba. Ba mu yarda da kyamar Yahudawa ba.”
Kungiyar Hamas da ke mulkin Gaza ta kaddamar da wani gagarumin harin ba-zata kan fararen hular Isra’ila a ranar Asabar.
Isra’ila ta mayar da martani da ci gaba da kai hare-hare ta sama kan yankin gabar teku mai yawan jama’a.
An kashe fiye da mutane 1,000 daga kowane bangare.