fidelitybank

Za mu daina kai dabbobi da kayan abinci Kudancin Najeriiya – Kungiya

Date:

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu fataucin dabbobi da kayan abinci ta Najeriya ta ce a shirye take ta daina safarar shanu da ma sauran kayan abinci zuwa kudancin ƙasar.

Ƙungiyar na mayar da martani ne a kan sanarwar da ƙungiyar ‘yan awaren Biafra ta IPOB ta fitar ranar Litinin, ta hana cin naman shanun da a ke shigarwa da shi daga arewacin ƙasar kama daga watan Afrilu.

A hira da BBC, shugaban ƙungiyar masu fataucin dabbobi da kayan abinci ta Najeriya Kwamared Muhammad Tahir, ya ce wannan mataki da IPOB ta dauka su ko a jikinsu.

“Muna son Najeriya ta zama kasa daya uwa daya al’umma daya, amma idan ya zamto su suna ganin hakan ta fi zame musu dai-dai to ai ta fi nono fari.” In ji Muhammad Tahir.

Ya kara da cewa ” wannan abun da ake kaiwa fa dukiya ce a ke kai musu ba tsiya ce a ke kai musu ba, abinci ne a ke kai musu ba guba ce a ke kai musu ba.”

“Saboda haka wanda ka ke kai ma wannan abinci ya ce ba ya kaunar wannan abincin sai ka ce dole ne lallai ko da yana kashe ka sai ka kai masa?”

Shugaban kungiyar masu fataucin kayan abincin daga Arewaci zuwa Kudancin Najeriyar ya jaddada cewa farfaganda ce kawai kuma “mun gaji da wannan farfaganda.

A cewarsa al’ummar Kudancin kasar ba za su iya juriyar ko da kwana daya ba a kai musu kayan abinci ko nama daga Arewacin Najeriya ba.

Dama ranar Litinin ne kungiyar da ke fafutukar ɓallewa daga Najeriya da son kafa Jamhuriyar Biafra wato IPOB, ta fitar da sanarwar haramta yin taken Najeriya da cin naman shanu da ake kai wa daga Arewa a wuraren bukukuwa da daukacin makarantun da ke Kudu maso gabashin kasar.

Kuma matakin daya ne daga cikin dokoki bakwai da IPOB ta sanar, da ta ce za ta fara aiwatar da su a 2022.

Daga ciki akwai kamfe don neman sakin fursunoninta da ake tsare da su wadanda ta ce ba su aikata wani laifi ba, da kuma batun fara zanga-zanga a manyan birane da ke fadin duniya.

Daga nan kuma ta bayyana cewa ta haramta cin naman shanu da kuma rera taken Najeriya kama daga watan Afrilun shekarar da aka shiga.

A baya yankin Kudancin Najeriyar ya fuskanci karanci da kuma tsadar kayan abinci da nama da ake shigarwa da su daga Arewacin kasar, a lokacin da kungiyar masu sayar da abincin ta shiga yajin aiki.

 

sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp