fidelitybank

Za mu ciyar da Tagwayen Kano gaba – Injiniya Hassan

Date:

Kungiyar Tagwaye ta kasa reshen jihar Kano ta gudanar da zaben shugabaninta karo na farko wanda za su jagoranci akalar ƙungiyar.

Shugaban kwamitin gudanar da zaben, Hassan Isah Muhd Gwale wanda ya jagoranci zaɓen ya tabbatar da Injiniya Hássan Ahamad Makari a matsayin sabon shugaban kungiyar, sai kuma Hassan Auwal Muhd Jak City ya zama mataimakin shugaba, yayin ds Hussaini Kabir Minjibir ya kasance a matsayin sakataren kungiyar.

Yayin ganawa da manema labarai, Hassan Isa Gwale ya bukaci wadanda su ka samu nasarar da su yi aiki tukuru, domin ciyar da kungiyar gaba.

Ya kuma bukaci wadanda basu samu nasara a zaben ba, da su marawa wadanda suka samu nasarar, domin ciyar da kungiyar gaba.

An dai gudanar da zaben ne a makarantar gidan Makama da ke ƙwaryar birnin jihar Kano, inda tagwaye mata da maza daga ƙananan hukumomi arba’in da hudu su ka halarci zaben.

Sabbin shugabannin dai a na sa ran za su tafiyar da harkokin kungiyar dai-dai da yadda kundin tsarin mulkin kungiyar ya tsara.

A Jawabinsa bayan rantsuwar kama aiki sabon shugaban kungiyar Tagwayen, Injiniya Hassan Ahmad Makeri, ya ce za su yi aiki tukuru tare da bujiro da sabbin dabarun da za su ciyar da kungiyar Tagwayen Kano gaba.

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Najeriya na neman dala biliyan 25 na bututun iskar gas zuwa Turai

Najeriya na neman dala biliyan 25 a matsayin kuɗin...

‘Yan sa-kai biyu ne suka mutu a harin da muka kai Zamfara – Sojoji

Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai...

Dakarun sojin ruwa a Najeriya sun yi kaɗan wajen tsaron ƙasa – Emmanuel Ogalla

Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya ya ce dakarunsa...

Juma’a da Litinin ranakun hutun Sallar Layya – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma'a da Liitnin masu...

Gwamnatin Neja zai haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man fetur

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya nemi aikin haɗin...

Tchiani ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da Nijar

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya...

An ceto yara 12 da aka yi safararsu a jihar Abia

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami'anta sun samu...

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...
X whatsapp