fidelitybank

Za mu cigaba da zanga-zanga saboda Tinubu ba shi da biyar magance matsalar mu – Ƙungiya

Date:

Ƙungiyar ‘The Take it Back Movement’, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka shirya zanga-zagar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya ta ce ”zanga-zangar za ta ci gaba”, duk kuwa da kiran dakatar da ita da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi.

Cikin jawabin da ya gabatar wa ƙasar ranar Lahadi da safe, shugaba Tinubu ya yi kira ga waɗanda suka shirya zanag-zangar su dakatar da ita tare da rungumar hanyar tattaunawa.

To sai cikin wani saƙo da ƙungiyar ‘The Take it Back Movement’ ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce shugaban bai taɓo buƙatunsu cikin jawabin nasa ba, sannna ya kasa ɗaukar alhakin ”kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zangar”.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International ta ce mutum 13 jamai’an tsaro suka kashe ranar Alhamis.

To sai rundunar ‘yansandan ƙasar ta musanta amfani da ƙarfin da ya wuce kima kan masu zanga-zangar, tana mai cewa mutum bakwai ne kawai suka mutu.

Rundunar ‘yansandan ta kama kusan mutum 700.

A ranar Lahadi wasu mutane da ake zargin ɓata-gari ne sun tarwatsa masu zanga-zangar a birnin Legas da ke kudancin ƙasar.

Masu zanga-zangar na buƙatar gwamnati ta mayar da tallafin man fetur da ta cire domin rage farashin fetur da na lantarki, haka kuma suna buƙatar hukumomin ƙasar su magance matsalar tsaro da cin hanci da rashawa.

Ana sa ran ci gaba da zanag-zangar a faɗin ƙasar har zuwa ranar Asabar mai zuwa.

Shugaban ƙasar dai ya umarci jami’an tsaro su ci gaba da tabbatar da doka da oda.

Yayin da ake fargabar samun ƙarin arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.

latest news in nigeria today 
2021 ripples

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp