fidelitybank

Za mu cigaba da yi wa Lebanon luguden wuta – Isra’ila

Date:

Isra’ila ta ce za ta cigaba da kai hare-hare kudancin Lebanon duk da kiraye-kirayen da shugabannin duniya suke yi a Babban Taron MDD na a tsagita wuta.

 

Ma’aikatar Lafiyar Lebanon ta ce an samu ƙarin mutuwar mutum shida a daren Talata, inda jimillar waɗanda suka rasu ya kai 560, tun bayan kaddamar da hare-hare da luguden wutar da Isra’ila ta fara ranar Litinin.

 

Isra’ila da Hezbollah sun tabbatar da kashe Ibrahim Qubaisi – wanda kwamandan Hezbollah ne da ya jagoranci harba makaman roka zuwa Isra’ila – ranar Talata.

 

Dubban ‘yan Lebanon ne suka tsere daga muhallansu tare da neman mafaka a makarantu da sansanonin da gwamnati ta samar.

 

Ofishin kare haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna damuwar kan adadin mutanen da aka kashe, inda ya ce akwai alamar yin watsi da dokokin aikin agaji na duniya.

 

A bangare guda Isra’ila ta nanata cewa dole ya sa take kai hare-hare a yankunan da ke da ɗimbin farar hula kamar Beirut, saboda Hezbollah na amfani da mutane a matsayin garkuwa.

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp