Sojojin Isra’ila sun ce za su zafafa hare-haren da suke kai wa Hezbollah a Lebanon, bayan luguden wutar da ta yi a ranar Litinin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane.
Ministan Lafiya na Lebanon Firass Abiad ya ce an kashe sama da mutane dari biyar da hamsin tun daga lokacin da Isra’ila ta fara ƙaddamar da hare-hare a ranar Litinin.
Ya ƙara da cewar mata da yara ƙanana kusan ɗari da hamsin na daga cikin waɗanda suka rasa rayukan nasu.
Mutane da dama na ci gaba da tserewa daga gidajensu a kudancin Lebanon
Wakiliyar BBC ta ce har yanzu Isra’ila ba ta bayyana wa’adin da za ta ɗauka tana ƙaddamar da hari ko kuma kai farmaki ta ƙasa ba, abin da ake ta hasashe a yanzu.
To sai dai Hezbollah ta bayyana cewar ta kai wa sojin Isra’la hare-hare a Arewacin Isra’ila.
Kasashen duniya sun sake yin kira da a kawo karshen faɗa tsakanin Isra’ila da Hezbollah.
Babban kwamishinan kare haƙƙin bil’adama a Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Turk, ya nemi dukkanin bangarorin da suke fada-a ji a yankin Gabas ta Tsakiya su taimaka a dakile rikicin.
Ma’aikatar harkokin wajen Chaina ta ce Beijing ta yi Allah Wadai da karya ka’idojin tsaron Lebanon.
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce bai kamata duniya ta ƙyale Isra’ila ta mayar da Lebanon wata Gaza ba.
Ya kuma kara da cewa Hezbollah, wadda Tehran ke goyon baya, ba za ta iya yaƙar Isra’ila ita kadai ba.