fidelitybank

Za mu cigaba da tunkudo da man fetur zuwa kasuwar duniya – OPEC

Date:

Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur da ƙawayenta ta OPEC+ ta amince da ci gaba da rage yawan gangar mai miliyan biyu daga kasuwar duniya duk rana.

Ƙungiyar ta sanar da matakin a yau Lahadi bayan kammala taronta karo na 34 ta bidiyo, wanda ministocin ƙasashen suka halarta.

Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan ƙasashen ƙungiyar G7 – mafiya girman tattalin arziki a duniya – sun ƙayyade farashin dala 60 kan kowace ganga ɗaya na man Rasha.

A ganawar da suka yi kafin yanzu, OPEC+ ta amince ta rage yawan man daga kasuwa da ganga miliyan biyu a kullum duk da kiraye-kirayen da Amurka ta dinga yi na kar ta yi hakan.

Ƙungiyar mai mamba 13 ta ce ba za ta janye matakin ba, “wanda aka ɗauka bayan lura da kasuwar a lokacin don ɗaukar matakin da ya zama dole da zimmar daidaita kasuwar fetur a duniya”.

OPEC ta sha nanata cewa ba za ta ɗauki ɓangare ba a yaƙin da Rasha, wadda mamba ce, take yi da Ukraine tana mai cewa ba ƙungiyar siyasa ba ce.

assu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp