fidelitybank

Za mu cigaba da kai tallafin abinci Nijar duk da alaƙa na neman yin tsami – Amurka

Date:

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce, Amurka za ta ci gaba da bayar da taimakon kayan agaji da tallafin abinci ga Jamhuriyar Nijar.

To sai dai Mista Blinken ya ce Amurka za ta dakatar da wasu tallafin da za su taimaka wa ƙasar da ke yammacin Afirka.

Ya ce Amurka za ta ci gaba da samar da tsaro don kare jami’anta da ke ƙasar.

Kalaman Mista Blinken na zuwa ne a daidai lokacin ƙasashen ƙungiyar Ecowas suka amince da amfani da ƙarfin soji a Nijar ɗin, matuƙar sojojin ba su mayar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki ba.

Tuni dai Nijar din ta sanar da janye jakadunta da ke wasu ƙasashen duniya ciki har da Amurka da faransa da kuma Najeriya.

A ranar Juma’a ne dai Najeriya ta sanar da rufe kan iyakokin ƙasar da Jamhuriyar ta Nijar, bayan katse wutar lantarki da take bai wa ƙasar, a wani mataki na tilasta wa. sojojin mayar da Bazoum kan mulki

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp