fidelitybank

Za mu ci gaba da rufe shagunan caca a Kano – Hisba

Date:

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta ce za ta ci gaba da bin tsarinta na rufe shagunan masu caca bayan hukunci wata kotu.

A ranar Juma’a kotun ƙolin ƙasar ta rushe dokar 2005, da ta amince da kafa hukumar kula da caca tare da halasta cacar wasanni a ƙasar.

Kotun ta ce hukuncin na nufin gwamnatocin jihohi ne ke da wuƙa da nama game da dokokin da suka shafi caca.

Daraktan hukumar Hisbah na jihar Kanon, Dakta Abba Sufi ya ce, hukuncin kotun na nufin hukumarsu za ta ci gaba da kai samame tare da rufe shagunan caca a faɗin jihar, saboda haramcin sana’ar a ƙarƙashin dokokin Musulunci.

Abba Sufi ya ce iyayen yara na yawan ƙorafi game da yadda yaransu ke ci gaba da faɗawa komar wannan mummunar sana’a a daidai lokacin da matsin rayuwa da talauci ke ƙaruwa tsakanin al’umma.

Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ake amfani da dokokin addinin Musulunci baya da dokokin ƙasa.

A watan da ya gabata hukumar Hisbar jihar ta kai samame tae da rufe gomman shagunan caca a faɗin birnin Kano.

To sai dai an dakatar da samamen sakamakon ƙarar da wasu ƙungiyoyi suka shigar, dogaro da cewa caca ba laifi ba ne a ƙarƙashin dokokin Najeriya.

latest nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp