fidelitybank

Za mu biya ƙarin albashin dubu 25 – Gwamnatin Tarayya

Date:

Gwmanatin tarayya ta ce, za ta ci gaba da bai wa ma’aikatan ƙasar ƙarin albashin wucin gadi na naira 25,000 a kowane wata har zuwa lokacin da za a kammala cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.

Cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai ranar Asabar a Abuja, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce wa’adin mafi ƙarancin albashi da aka yi a shekarar 2019 ya ƙare ne ranar, 8 ga watan Afrilun 2024.

A ranar juma’a ne dai ƙungiyoyin ƙwadogon ƙasar suka ce za su tsunduma yajin aiki daga gobe Litinin, kasancewar wa’adin ranar 31 ga watan Mayu da suka bai wa gwamnati na amincewa da mafi ƙarancin albashi ya wuce ba tare da cimma matsaya ba.

Gwamnatin ta ce amince da biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙasar, to amma haɗakar ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun yi watsi da wannan ƙari, inda suka buƙaci gwamnati ta biya raira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai shugaban ƙasar ya yi wata ganawa da jagororin gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon bayan da suka yi barazanar shiga yajin aiki kan matakin shugaban na cire tallafin man fetur.

A lokacin ganawar shugaba Tinubu ya yi musu alƙawura da dama ciki har da amincewa da ƙarin albashin wucin gadi na Naira 25,000 ga kowane ma’aikaci, har tsawon wata shida, kafin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi.

Kan haka ne ministan yaɗa labaran ya ce kasancewar har yanzu ba a kammala cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin ba, gwamnati za ta ci gaba da bayar da wannan ƙari har zuwa lokacin da za a cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin.

”Alƙwarin gwamnatin tarayya na yi wa ma’aikata ƙari a albashinsu na wata shida, ba zai dakata ba har sai an kammala cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi”, in ji ministan

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta ɓullo da wannan tallafi ga ma’aikatan ƙasar ne domin tabbatar da cewa ba su galabaita ba, kafin cimma matsaya a kan mafi ƙarancin albashin.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp