fidelitybank

Za mu binciki zafin wariyar launin fatar da aka yi wa Lamine – Real Madrid

Date:

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta buɗe bincike kan cin zarafin wariyar launin fata da ake zargin an yi wa matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, a wasan El-Clasico da aka buga ranar Asabar a Bernabeu.

Bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wani bangare na magoya bayan Madrid suna furta kalamun ɓatanci kan ɗan kasar Sifaniyan mai shekaru 17 da haihuwa yayin da yake murnar ƙwallon da ya ci a minti na 77.

Sanarwar da Real Madrid ta fitar ta ce: “Real Madrid ta yi kakkausar suka ga duk wani nau’in halayya da ya shafi nuna wariyar launin fata, da kyamar baƙi ko tashin hankali a fagen ƙwallon ƙafa da wasanni, kuma ta yi matukar baƙin cikin cin mutuncin da wasu tsirarun magoya bayan ƙungiyar suka yi a daren asabar a wani ɓangare na filin wasan.”

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya (RFEF) da La Liga sun ɗauki matakai don magance ƙaruwar cin zarafin wariyar launin fata wanda suka haɗa da rufe wani ɓangare na filin wasa.

A makon da ya gabata, an kama wasu mutane huɗu bisa zarginsu da gudanar da wani gangami a shafukan intanet domin nuna ƙyama da wariyar launin fata a kan ɗan wasan Real Madrid Vinicius Jr.

Haka kuma an yanke wa wasu magoya bayan Valencia uku hukuncin ɗaurin watanni takwas a gidan yari a watan Yuni. saboda cin zarafin ɗan wasan gaban na Madrid a wani wasa a watan Mayun 2023.

pulse news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp