fidelitybank

Za mu bincika cin zarafin da aka yi wa Daliba a Ekiti – ‘Yan Sanda

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta ce, ba ta da masaniya kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna yadda wata dalibar jami’ar ilimi da kimiya da fasaha ta Bamidele Olumilua, Ikere take cin zalin wata ɗaliba ƴar uwarta a wani wuri mai kama da daji.

Rundunar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.

“Wannan sanarwar na son sanar da ƴan Najeriya da kuma mutanen jihar Ekit cewa rundunar ‘yan sandan jihar ba ta da masaniya kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna wata ɗalibar jami’ar jihar, BOUESTI tana cin zalin ɗaliba ƴar uwarta.” in ji sanarwar.

“Rundunar ta bayyana irin wannan cin zalin a matsayin rashin mutuntaka kuma ba za a yarda da shi ba.”

Rundunar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Ekiti, CP Akinwale Kunle Adeniran ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin domin tuni ya umurci kwamandan yankin Ikere da ya haɗa kai da hukumar gudanarwar jami’ar tare da tabbatar da an gano wadda ta aikata wannan laifin don fuskantar sakamakon shari’a.

Sanarwar ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu kuma su guji daukar doka a hannunsu domin ana daukar matakan da suka dace.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp