Hukumar zaɓe INEC, ta ce za ta binciki zargin rubuta alƙaluman da ba na gaskiya ba a wasu rumfunar zaɓen gwamnan jihar Edo da aka hudanar ranar Laraba.
Cikin wata sanarwa ta hukumar ta fitar a shafinta na X, ranar Asabar da daddare, INEC ɗin ta sha alwashin gudanar da cikakken bincike kan zargin shigar da alƙaluman sakamakon da ba na gaskiya a takardar rubuta sakamako a wasu rumfunan za ben jihar.
“Wannan shi ne karo na biyu da muke samun irin wannan ƙorafi a cikin rumfunan zaɓe 4,519 da aka gudanar da zaɓen. Don haka hukumarmu za ta ɗauki matakin bincike cikin gaggawa kan lamarin, tare da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu da hannu a ciki,’’ kamar yadda sanarar ta yi ƙarin haske.
A yanzu dai hankula sun karkarta birnin Benin, babban birnin jiran inda ake jiran dakon fara karɓar sakamakon zaɓen daga ƙanannan hukumomin jihar 18.
Bayanai da aka tattara daga rumfunan zaɓe na nuna cewa ‘yan takara biyu na PDP mai mulkin jihar da APC mai mulkin Najeriya ne ke kankankan a zaɓen.
Shi dai ɗan takarar PDP na samun goyon bayan gwamnan jihar, yayin da na APC ke samun goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasar.