Gwamnatin tarayya ta sha alwashin bin kadin kisan da aka yi wa wani dalibi dan Najeriya mai shekara 19 da ke karatu a kasar Canada. Rahotanni sun bayyana ana zargin ‘yan sandan Canada ne sukai ajalin matashin.
Shugaban hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (Nidcom) Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana zargin kisan dalibin a Manitoba a Canada da rashin imani.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar 4 ga watan Junairu 2024, dauke da sa hannun maimagan da yawun ofishin Abike ta ce za su tabbatar an yi wa mamacin adalci.
Sanarwar ta kara da kira ga hukumomin kasar Canada da tuni suka ce sun fara gudanar da bincike kan lamari su ta bbatar an yi shi cikin adalci.
Sun mika sakon ta’aziyya ga iyaye da ‘yan uwa da aboakan dalibi Folabi, tare da fatan Allah ya sa bakin wuyarsa kenan.
Yadda Folade ya gamu da ajalinsa
Kamar yadda Nidcom ta fitar da sanarwa, bayanan da suka samu sun nuna dan sanda ne ya harbi matashin dan Najeriya mai shekaru 19 a ranar 31 ga watan Disamba 2023, gabannin shiga sabuwar shekarar 2024 a yankin Manitoba da ke Canada.
Duk da cewa babu cikakkun bayanai kan mutuwarsa, amma hukumar ‘yan sandan Monitoba sun wallafa takaitaccen bayani a shafinsu na intanet na cewa ” sun ce an kira ‘yan sandan ta wayar tarho, akan wani matashi da ya ke abu kamar maras hankali.”
‘Yan sandan sun ce su na isa wurin, duk kokarin da suka yi domin shawo kan matashin ya ci tura, dalilin da ya sa ‘yan sandan sukai harbi kenan bisa tsautsayi ya yi ajalinsa.”


