Sabon ƙaramin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle, ya ce, shi da takwaransa ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, za su bai wa maraɗa ƙunya a ɓangaren samar da tsaro a Najeriya.
Yayin da yake jawabi a wani taron liyafa da aka shirya masa don taya shi murnar samun matsayin a Abuja, Matawalle ya ce ya yi ta jin bayanai ana ta cewa shi da Badaru ba su da ƙwarewar da za su iya magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Tsohon gwamnan na jihar zamfara ya ce masu faɗin wannan magana ba su ma san me ake nufi da tsaro ba.
”To ba a nan gizo ke saƙar ba, domin kuwa za ka iya haifar ɗa, amma ya fi ka ƙwazo, ya fi ka hazaƙa, sannan ya fi ka ilimi”.
Matawalle ya ce a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara babu abin da bai yi ba, domin daƙile matsalar tsaron da jihar ke fuskanta, inda ya ce an kwashe lokaci mai tsawo ba tare da samun labarin faruwar wani abu na tayar da hankali a jihar ba.
Ƙaramin ministan tsaron ya ce ya ɓullo da matakai da dabarun yaƙi da ‘yan bindiga a lokacin da yake gwamnan jihar ta Zamfara.
”Duk matakan da na riƙa ɗauka domin magance matsalar tsaro a zamfara, sai na yi wasu gwamnoni su ɗauka”.
Bello Matawalle na daga cikin ministocin da za su fuskanci babban ƙalubale a ma’aikatunsu, sakamakon yadda tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar, kama daga ayyukan ‘yan fashin daji a arewa maso yamma, da Boko Haram a arewa maso gabas, ga kuma matsalar ‘yan awaren IPOB a yankin kudu maso gabashin ƙasar.


