Amurka ta ce, za ta ƙyale ƙawayenta na Nahiyar Turai su bai wa Ukraine jirgin yaƙin da ta ƙera na F-16.
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaro, Jake Sullivan, ya ce Shugaba Joe Biden “ya faɗa wa taron ƙasashen G7 [na mafiya girman tattalin arziki a duniya]” game da matakin yayin taron da suke gudanarwa a Japan yanzu haka.
Sojojin Amurka za su bai wa na Ukraine horo kan yadda za su yi amfani da jiragen, in ji Mista Sullivan.
Ukraine ta daɗe tana neman manyan makamai na zamani daga ƙawayen nata, kuma Shugaba Volodymyr Zelensky ya yabi matakin da cewa “mai cike da tarihi”.
Ƙasashen da suka mallaki irin waɗannan makamai ko jirage ba za su iya sayarwa ko kuma kai su wata ƙasa ba sai da amincewar Amurka.