Shugaba Bola Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta fara raba wa masu karamin karfi naira miliyan 15 a watan Oktoban da muke ciki.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, lokacin da yake jawabi ga ƴan ƙasar don murnar bikin cika shekara 63 da samun ƴancin kai.
Ya ce “Daga watan nan, za mu faɗaɗa shirinmu na tallafa wa al’umma ta hanyar raba wa magidanta ƙarin miliyan 15.
“Za mu yi haka ne domin bunƙasa aikin yi, za mu kuma samarwa masakaita da ƙananan masana’antu masu zuba jari domin ciyar da su gaba,” in ji Tinubu.