Cibiyar tallafi ta Sarki Salman na Saudiyya ta ce za ta ɗauki nauyin raba tagwayen da aka haifa manne da juna a jihar Kano.
Tuni Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya raka Hassana da Hussaina zuwa filin jirgin sama na Aminu Kano, inda aka tafi da su Saudiyyar a yau Litinin.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa jariran suna haɗe ne ta ƙirji kuma sun haɗa wasu gaɓoɓin masu muhimmanci.
“King Salman Humanitarian Aid and Relief Centre (KSARelief) da haɗin gwiwar wasu sanannun likitocin fiɗa na yunƙurin tallafa wa waɗannan yara don su yi rayuwa mai kyau a nan gaba,” a cewar wata sanarwa daga ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a gudanar da tiyatar ne a cibiyar King Abdulaziz Medical City da ke birnin Riyadh.