fidelitybank

Za mu ɗauki mataki mai tsauri a kan masu kisan gilla a Zamfara – Buhari

Date:

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya buƙaci al’ummomin da ƴan bindiga su ka yi wa kisan gilla a Jihar Zamfara, da su ƙara haƙuri cewa za su gano waɗanda su ka aikata wannan mummunan aiki tare da ɗaukar mataki mai tsauri a kansu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce, Buhari ya nuna ɓacin ransa matuƙa dangane da rahoton da ya samu kan kisan gillan da a ka yi, inda ya ce shure-shure ne ƴan bindigan su ke yi wanda bai hana su mutuwa, ganin cewa suna fuskantar matsin lamba daga sojoji waɗanda a ka inganta da makamai, domin yaƙar ƴan bindigar.

Shugaba Buharin ya sake tabbatar da cewa, “Ƴan bindigar na daf da zama tarihi a Najeriya, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba a yaƙin da mu ke yi da waɗannan mutanen da su ka addabi jama’ar da ba su ji ba su gani ba”. Buhari

Jihar Zamfara dai fama da hare-hare daga harin ƴan ta’adda, domin kuwa ko a kwanan nan ƙananan hukumomin Anka da Bukuyyum da ke Jihar su ka tabbatar da binne mutum 143 sakamakon harin da ya rutsa da su.

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp