Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta ce, za ta kakabawa gidajen mai da ke sauya fanfunan mai.
Farouk Ahmed, Shugaban Hukumar NMDPRA ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da kwamishinonin Hukumar tattara kudaden shiga da kasafi (RMAFC) ranar Juma’a a Abuja.
Ahmed ya ce gidajen man da aka kama suna rarraba mai tare da gyaran famfunan mai za su fuskanci tsauraran takunkumi, da suka hada da soke lasisin aiki, dakatarwa daga aiki, ko kuma rufewa, ya danganta da girman laifin.
A cewarsa, gyaran fanfunan mai da masu gidajen mai ke yi, babban abin damuwa ne ga hukumomin kula da mai da kuma gwamnatin tarayya.
“Abin da muke yi a yanzu shi ne, muna da wasu ma’aikatanmu da ke zagayawa domin yin bincike a kan wasu gidajen mai. Idan ka shiga tasha ka fita, ba za ka san ko an yaudare ka ba sai ka yi awo.
“Wani lokaci muna yin awo na jiki inda muke zuwa wasu tashoshi mu sayi lita daya mu duba wannan muhallin mu ga ko da gaske wannan lita daya ce. Daga nan za mu san ko sun yi wa famfo ne ko a’a,” inji shi.
Shugaban NMDPRA ya ce hukumar za ta ci gaba da hada kai da RMAFC domin samar da karin kudaden shiga ga hukumar.
“Mun fara aikin, amma wannan hadin gwiwa ne kawai a kan bangarorin da za mu iya inganta samar da kudaden shiga ga tarayya. Akwai fannoni guda biyu da ya kamata mu duba, ko dai don samar da kudaden shiga ko rage kashe kudi,” inji shi.
Ya yi kira ga ‘yan kasa da su saka hannun jari a bangaren tattalin arziki mai tsaka-tsaki, yana mai cewa: “Misali, idan kuna son gina masana’antar iskar gas, ku zo wurinmu; za mu ba ku jagorori da manufofi, kuma za ku zo ku saka hannun jari. Yankin da kake son saka hannun jari zai ƙayyade farashin zuba jari; da damar zuba jari a can.”
Shugaban RMAFC, Mista Bello Shehu, ya ce makasudin kulla alaka tsakanin kungiyoyin biyu shi ne karfafa hadin gwiwarsu.


