Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ambato Hasan Haghigian, babban jami’in mulki na jihar Gabashin Azerbaijan, yana cewa za a gudanar da jana’izar Ebrahim Raisi da sauran abokan tafiyarsa a gobe Talata.
Za a yi jana’izar ce a Tabriz, a cewar rahoton.
Ya ce ana kan aikin kai gawar tasu zuwa Tabriz amma za a kai su cibiyar gwajin lafiya tukunna.