Hukumar zaɓe ta INEC, ta ce, nan gaba cikin wannan wata za ta fara yin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar gabanin zaɓukan 2027.
Cikin wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, ta ce za ta fara rajistar masu zaɓen ta yanar gizo a ranar 18 gawatn Agustan da muke ciki.
Hukumar zaɓen ta kuma saka ranar Litinin 25 ga watan Agustan a matsayin ranar fara rajistar a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi da sauran wuraren da ta ware don gudanar da aikin.
INEC ta ce za a riƙa gudanar da aikin ne daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Juma’a.
Kan hakan ne hukumar ta buƙaci waɗanda ba su da rajistar su yi amfani da damar wajen mallakar rajistar.
Hukumar ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun yin rajistar zaɓe a Najeriya.