Sabon shugaban riƙo na ƙasar Syria ya ce ƙasar za ta kwashe shekara uku kafin rubuta sabon kundin tsarin mulki, sannan shekara huɗu kafin shirya zaɓe.
Yayin wata hira da kafofofin yaɗa labaran Larabawa, Ahmad al-Sharaa ya ce za a shafe shekara guda kafin ‘yan ƙasar suka ga wani sauyi na zahiri a ƙasar, bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad.
Ya ƙara da cewa zai soke ƙungiyarsa ta H-T-S da ta jagorancin kifar da gwamnatin Assad a taron tattaunawa na ƙasa da za a shirya nan gaba.
Taron shi ne na farko da za a fara auna ko sabuwar gwamnatin za ta cimma alƙawuran da ta ɗaukar wa ‘yan ƙasa na haɗa kan al’umma bayan shafe shekara 13 ana yaƙin basasa.
Mista al-Sharaa ya sha cewa baya ganin kansa a matsayin wanda ya ceci ƙasar, yana haƙƙaƙe cewa ‘yan ƙasa ne suka ceci kansu.