Hukumar Alhazan Najeriya ta ce za ta kammala kwashe mahajjatanta da suka je aikin Hajji na bana a yau Talata daga Saudiyya.
“Jimillar mahajjatan jihar Kwara 312 ne za su isa birnin Ilorin a jirgin kamfanin Air Peace,” in ji hukumar Nahcon cikin wata sanarwa a yau Talata.
Jirgin nasu zai zama jigila ta 119 kuma ta ƙarshe da suka yi aikin mayar da ‘yan Najeriya gida bayan kammala aikin Hajjin na bana.
Nahcon ta ce za ta kammala aikin ne kwana uku kafin cikar wa’adin da ta tsara yin hakan.
Jimillar mutum 47,171 hukumar ta kai Saudiyya cikin kwana 27, sannan ta dawo da alhazai 50,091 cikin kwana 25.
Alhazan Najeriya da dama sun yi ƙorafi game da abincin da aka dinga ba su yayin zamansu a Saudiyyar.


