Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMET), ta yi gargadin cewa, yanayin zafi a wasu biranen Najeriya zai tashi sama da yadda aka saba nan da kwanaki masu zuwa.
NiMET a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta bayyana cewa, ana sa ran za a iya samun zafi sama da digiri 40 nan da sa’o’i 48 masu zuwa inda ake sa ran za a fuskanci matsanancin zafi a sassan Kebbi, Sokoto, Zamfara, Taraba, da Adamawa.
Ya ce galibin sassan garuruwan Arewa ana sa ran za su yi zafi tsakanin digiri 35 zuwa 40.
Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa garuruwa irinsu Bauchi, Gombe, Borno da Yola na fuskantar barazanar fuskantar matsanancin zafi.
Don haka hukumar ta shawarci mutanen da ke irin wadannan wurare da su rika shan ruwa mai yawa a cikin wannan lokaci domin gujewa rashin ruwa, inda ta ba da tabbacin ci gaba da lura da yanayin da kuma sabunta ‘yan Najeriya yadda ya kamata.