fidelitybank

Za a yi zafin rana sosai a Kano da wasu jihohi – NIMET

Date:

Hukumar kula da yanayi ta kasa NIMET, ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan kare lafiya ba, to akwai yiyuwar mazauna Abuja, Kano, da sauran jihohin Arewa da dama za su fuskanci tsananin zafi wanda zai shafi lafiyarsu.

Tsananin zafi dai na janyo cutuka da dama waɗanda za su iya kai wa mutuwa, kuma hakan a faruwa ne a lokacin da jiki ya kasa sarrafa zafin.

Mazauna waɗannan jihohin na iya fuskantar matsanancin zafi, wanda zai sa su shiga yanayi mara kyau, a cewar Nimet.

“Mun sake shiga lokacin zafi. Ya kamata jama’a su ɗauki matakan da suka dace,” kamar yadda “NiMET ta yi gargaɗi.

Ta ce Abuja, Kano, Sokoto, da Kogi ne za su fi fuskantar tsananin zafi, inda ta shawarci mazauna yankunan da su ɗauki matakin kariya da ya kamata.

Wasu jihohin da ke cikin rukunin fuskantar zafin sun haɗa da Kebbi, Katsina, Adamawa, Gombe, Bauchi, Taraba, Neja, Zamfara, Nasarawa, Jigawa, Benue, da kuma Kwara.

NiMET ta kuma gargaɗi mazauna jihohin Osun, Ekiti, Ondo, Bayelsa, Akwa Ibom, Anambra, Delta, Enugu, Edo, Ogun, Plateau, Borno, Imo, Abia, da Cross River da cewa su kasance cikin shiri don karuwar zafi, duk da cewa zafin ba zai yi tsanani ba kamar na sauran jihohi.

today nation

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp