Hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za’a gudanar da zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni na shekarar 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya sanar da hakan a hira da manema labarai ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, za’a gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 25 ga watan Febrairu, 2023.
Yayinda na gwamnoni da majalisar dokkin jiha zasu gudana ranar Asabar, 11 ga Maris, 2023.
Yakubu ya ce, wannan sabon rana ya yi daidai da ka’idojin da doka ta gindaya na sanar da ranar zabe a na saura akalla kwanaki 260 da ranar zabe.