Hukumar zaɓe INEC, ta ce, sai a gobe ne za ta gudanar da zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun jiha a ƙaramar hukumar Kwande ta jihar Benue.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce a baya ta ɗage zaɓen da aka tsara gudanarwar ranar Asabar 18 ga wata, bayan da aka samu cuɗanyar muhimman takardun zaɓe tsakanin gundumomin majalisar dokokin jiha biyu da ke ƙaramar hukumar.
Kan haka ne hukumar ta ce ta tuntuɓi wakilan jam’iyyu da sauran masu ruwa da tsaki domin sake sanya sabuwar ranar da za a gudanar da zaɓen.
Karanta Wannan: INEC na kokarin murde zaben Adamawa – Atiku
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a yanzu hukumar ta saka gobe Talata 21 ga watan Maris a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen a ƙaramar hukumar.
Daga ƙarshe hukumar ta yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a a yankin da su fito domin zaɓar mutanen da suke so a zaɓen da za a gudanar goben.