Gawar Fafaroma Francis ta isa Cocin St Peter’s Basilica, inda za a ajiye ta domin yi mata bankwana.
Za a fara da gudanar da addu’o’i tukuna, kafin a bar masu makoki su fara wucewa ta gaban akwatin gawar domin girmamawa da sallama da babban limamin mabiya darikar ta Katolika na duniya.
Gawar za ta kasance a cocin na St Peter’s Basilica na tsahon kwanaki uku, kafin ayi jana’iza a binne shi a ranar Asabar.
A harabar cocin tuni mutane suka taru domin samun yin bankwana da gawar.
Haka zalika an fara shirye-shirye da karbar baÆ™uncin dubban mabiya da wakilan akalla kasashe 100 da za su halarci jana’izar.
An dai tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen birnin Roma.