Gwamnatin Tarayya za ta jagoranci gudanar da taron addu’o’i ga tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Muhammadu Buhari a babban masallacin Juma’a na ƙasa da ke Abuja.
Fadar shugaban ƙasar ce ta shirya taron domin addu’o’in neman gafara wa tshon shugaban ƙasar.
Ana sa ran manyan jami’an gwamnati za su halarci taron addu’o’in.
A ranar Alhamis ne aka gudanar da taron addu’o’i da karramawa da musamman ga tsohon shugaban ƙasar a fadar gwamnatin ƙasar.