Masoyan siyasar Kano sun shiga cikin damuwa a ranar Juma’a, bayan rahotannin da ke cewa, Bashir I. Bashir, dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour a zaben 2023 na fuskantar tiyatar zuciya a wani cibiyar kiwon lafiya da ba a bayyana sunansa ba a ketare.
Bashir, ta hanyar tabbatar da hakan a shafin sa na Facebook, ya yada labarin ciwonsa ga masoya da masu binsa baki daya.
Saƙon na sa ya ce, “Yan’uwa ina bukatar addu’o’inku! A kan aikin zuciya da za a yi min.”
Dan siyasar nan mai tausasawa, haifaffen Kano ya bayyana cewa: “Na kawo matata Asibiti, amma ni ne aka same ni da wani abu da ke bukatar kulawa cikin gaggawa.”
Ɗan siyasar ya koka da cewa: “Zuciyata na zubar da jini yayin da irin wadannan matsalolin kiwon lafiya ba za a iya magance su yadda ya kamata ba a asibitocin gwamnati. “
Ya ce “Najeriya babbar kasa ce, da damammaki marasa iyaka. 2023 ya kamata ya zama shekarar da dukkanmu muka yanke shawara mu zabi shugabanci na gari mai inganci. “
An san Bashir da furucinsa a fili cewa, “Muna sake haduwa idan na fito. Idan ban yi ba, ya kamata matasa su ci gaba daga inda muka tsaya. Allah ya jikan mu da rahama.”


